Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : bayyana cewa tawagar sojojin kasar Faransa wacce ta fito daga kasar Burkina Fasso ta gamu da fushin masu zanga-zangar nuna rashin amincewar da samuwar sojojin faransa a yankin ne a jiya jumma inda suke korafin cewa sojojin na Faransa sun kasa magance matsalolin tsaro nay an ta’adda a yankin nasu.
Labarin ya kara da cewa kafin haka tawagar sojojin na Faransa sun kwace mako guda masu zanga zanga sun hana su wucewa a gabacin Burkina fashi a yankin da yan ta’adda suke cin karansu ba babbaka duk tare da samuwar sojojin faransa a kasar.
Ko a makon da ya gabata ma daruruwan yan kasar Burkina sun hana tawagar sojojin kasar Faransa wucewa daga karin kaya a cikin kasar zuwa kasar Mali.
Sojojin Faransa sun yi amfani da karfi don budewa kansu hanya a garin Tera inda suka kwana wanda yay i sanadiyyar mutuwar mutane biyu da kuma raunata wasu 18.
342/